Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sallami Yusuf Buhari Daga Asibiti


Yusuf Buhari

Mai baiwa shugaba Buhari shawara kan harkokin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa an sallami Yusuf Buhari wanda aka kwantar da shi a asibitin Cedarcrest da ke Abuja bayan hadarin babur da yayi.

A wata sanarwa ga manema labarai na Asibitin Cedarcrest da shi Ahmad din ya saka a shafinsa, ya bayyana cewa an sallame Yusuf yau bayan kulawan da ya samu a asibitin. Hakan kuma ya nuna cewa akwai kayan aiki da ake bukata na zamani don kula da marar lafiya a kasar wanda ba sai an kai shi wata kasa ba.

Haka zalika sun musanta wasu maganganu da ake ta yadawa cewa har da wani abokin Yusuf Buhari a hadarin da ya auku inda suka ce shi kadai ne akan babur dinsa. Kuma Aisha Buhari ba ta kwanta asibiti ba kamar yadda ake cewa tayi bayan ganin halin da danta ya shiga.

Asibitin kuma ya karyata batun cewa an rufe ganin marar lafiya tun bayan da aka kwantar da dan shugaban kasar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG