Accessibility links

Za a Ci Gaba Da Zabe A Wadansu Mazabu Yau A Ghana


Wani yana wucewa kusa da hotunan 'yan takara a Ghana
Hukumar zabe ta kasar Ghana ta kara lokacin kada kuri’a a babban zabe na kasa da aka gudanar jiya inda wadanda basu iya kada kuri’a ba, sakamakon wadansu muhimman dalilai zasu je su jefa kuri’unsu.

Kwamishinan zabe na kasar Ghana ya bayyana cewa, za a ci gaba da gudanar da zabe yau asabar a wadansu runfuna sakamakon tangarda da aka samu da wadansu na’urorin da suka hana masu kada kuria da dama yin zabe.

Wannan ne karon farko da hukumar zaben kasar Ghana take amfani da wani sabon salo inda injuna suke tantance masu rajista ta wajen gwada yatsunsu.
An ci gaba da kirga kuri’u a mazabun da ba a sami tangarda ba.
XS
SM
MD
LG