Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Fara Tattaunawa Tsakanin Korea Ta Arewa da Majilisar Dinkin Duniya


North Korea leader with rockets and kids
North Korea leader with rockets and kids

Ana iya cewa an fara samo bakin warware matsalar dake tsakanin Korea ta Arewa da Majilisar Dinkin Duniya, domin ko sun amince su rika tattauna lokaci-lokaci

Kasar Korea ta Arewa ta aminice su rika tattaunawa kai a kai da MDD.

Kafar yada labarai na kasar ta Korea ta Arewa ya fada yau asabar cewa an cimma wannan matsayar ce biyo bayan ziyarar da wani babban jamiin MDD yakai a kasar ta Korea ta Arewa.

Jeffrey Feltman wanda shine karamin Sakataren MDD mai kula da harkokin demokaradiyya, shine ya ziyarci kasar ta Korea ta Arewa a cikin wannan satin inda ya gana da wasu jamiian gwamnatin kasar da suka hada da ministan harkokin waje Ri Yoing Ho da mataimakin sa Pak Myong Guk.

Wannan ziyarar ta Feltman ta kara bada gudun mowa wajen nemo bakin warware matsalar dake tsakanin kasar da MDD.

Wannan ziyara Feltman tazo ne dai, dai-dai da lokacin da Amurka da kasar ta Koriya ta Arewa suka kaddamar da atisayen su mafi girma.

Dama da ita kasar ta Korea ta Arewa Amurka sun fara kai wa juna wuya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG