Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Fara Damke Direbobin Dake Lodi Fiye Da ‘Kima a Adamawa


Jami'in Hukumar Kare Hadurra Alhaji Idris Fika
Jami'in Hukumar Kare Hadurra Alhaji Idris Fika

Biyo bayan wani mummunan hadarin mota da ya faru a jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya inda fiye da mutum 50 suka mutu da kuma dabbobi, yanzu haka hukumomi kiyaye hadurra na barazanar damke duk wani direban babbar mota da ya ‘dauki fasinjoji fiye da ka’ida, tare da daukan matakan hana hawan bel-bela da ake yi akan manyan motoci.

Wannan kuma na zuwa ne yayin da hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ke shirin fara amfani da na’urar takaita gudu wato speed meter, batun da yanzu ke cigaba da jawo cece-kuce a kasar.

Shi dai wannan sabon mataki da hukumomi ke shirin dauka a yanzu, yana daga cikin gabaren matakan rage munanan hadurra da ake yawaitar samu a kasar, kasancewar a karshen makon da ya gabata ma wani mummunan hadarin mota yayi sanadiyyar rayuka, a kusa da garin Ngurore dake jihar Adamawa, yayin da dinbin mutane cikin babbar motar dakon kaya ke komowa gida daga kasuwar garin Song.

Wani da hatsarin mota ya rutsa da shi a Adamawa
Wani da hatsarin mota ya rutsa da shi a Adamawa

Da yake karin haske game da wannan sabon mataki da hukumomin kare hadurra ke shirin dauka na hana hawan bel-bela, jami’in kula da sintiri da ayyukan ko ta kwana na hukumar ta Road Safety a shiyar Adamawa, Alhaji Idris Fika, ya ce daukan wannan mataki ya zama dole ganin yadda rayuka ke salwanta a kullum, sakamakon ganganci da wuce-ka-ida da direbobi ke yi musamman na manyan motoci.

Yanzu haka dai tuni jama’a suka fara maida martini game da wannan sabon matakin da hukumomin ke shirin dauka, inda wasu ke yabawa, wasu kuma ke ganin talauci ke sa wuce ka’idar.

A na su martanin, kungiyoyin direbobi a Najeriya na ganin matakin yayi dai dai. Alhaji Bello Adamu Ngurore, dake zama shugaban kungiyar direbobi ta NURTW reshen jihar Adamawa, ya ce za su bada hadin kai don kwalliya ta biya kudin sabulu.

Baya ga matsalar lalacewar hanya a Najeriya, wasu matsalolin dakan jawo munanan hadurra sun hada da tukin gangaji da kuma hawan kawarar da ake yi wa ababen hawa wanda daga baya kan jawo da-na-sani.

Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG