Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Kashe Naira Miliyan 4 Kan Ciwon Tarin Fuka A Jihar Kebbi


Wata mai fama da cutar tarin fuka

Ofishin rigakafin tarin fuka da kuturta na kasa yace za a kashe naira miliyan hudu, domin su fadada kiyaye ciwon tarin fuka a kananan hukumomi 15 na jihar kebbi.

Ofishin rigakafin tarin fuka da kuturta na kasa yace za a kashe naira miliyan hudu, domin su fadada kiyaye ciwon tarin fuka a kananan hukumomi 15 na jihar kebbi.

Shugaban shirin na kasa, Mr. Pius Sunday ne ya bayyana haka a cikin wata hira ga manema labarai a wata ziyara da ya kai birnin Kebbi.

Bisa ga cewarshi, za a samar da dakunan bincike 15 karkashin shirin, inda za’a ajiye magunguna a kuma rika jinyar wadanda suke fama da cutar.

Mr. Pius Sunday ya bayyana cewa, za a rika yiwa masu fama da cututukan jinya kyauta. Kuma tuni aka jihar magungunan ciwon tarin fuka.

Shugaban yaki da cutar ya gargadi masu fama da cutar su rika zuwa domin shan magani domin maganin ciwon da yace yana da muni da ake iya warkarwa.

Mutane 400 ne yanzu suke shan magani a dakunan shan magani dabam dabam na jihar.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG