Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Sake Mayar Da Takunkumi Kan Iran


Sakataren ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo yace tilas kasar Iran ta fara nuna abinda ya kira "abinda ya dace da kasa,'' yayin da Amurka ke kokarin sake kakabawa Terhan takunkumi.

Pompeo ya gayawa manema labarai jiya Lahadi cewa , wannan ya shafi yaddda al'ummar kasar Iran bata jin dadin gwamnatinta kuma shugaba Trump ya fayyace haka karara. Muna son alummar Iran su kasance sun da murya mai karfi kan wanda zai zama shugaban su.

Ya ce fadar White House zata bada cikakken bayani yau Litinin nan kan takunkumin da za'a sanya wanda kuma zai fara aiki gobe Talata kan kamfaninnikan Iran, da suka hada da kamafonin kera motoci, gwal, kwal da karafu.

Ya kara da cewa, ba za'a bar Iran ta kara sayan jiragen Amurka ko na igila ba. An kuma ba daidaikun al'umma da kuma harkokin kasuwanfci dake hulda da wadannan kamfanonin wa'adin kwanaki casa'in su dakatar da ayyukan su. Yau litinin Wa'adin ya cika.

Iran ta sha musunta cewa tana gudanar da ayyukan nukiliyarta da nufin kera makaman nukiliya .

Facebook Forum

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG