Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Turawa Shugaba Tinubu Kudurin Kafa Hukumar Kula Da Arewa Maso Yamma - Jibrin

Barau Jibrin dai shi ya dau nauyin kudurin wanda Majalisar Dattawa da Wakilai suka amince da shi don kawo dauki ga magance kalubalen da ke addabar yankin na tsaro.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Jibrin Barau, ya ce nan ba da dadewa za a turawa Shugaba Tinubu kudurin kafa hukumar kula da raya arewa maso yamma.

Barau Jibrin dai shi ya dau nauyin kudurin wanda Majalisar Dattawa da Wakilai suka amince da shi don kawo dauki ga magance kalubalen da ke addabar yankin na tsaro.

Jihohn yankin 7 sun hada da Kaduna, Katsina, Kebbi, Kano, Jigawa, Sokoto da kuma Zamfara.

An ruwaito Barau Jibrin na nuna kwarin guiwar cewa shugaba Tinubu zai amince da kudurin inda ya godewa majalisun biyu don marawa kudurin baya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG