Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a yiwa wata mata matashiya ‘yar kasar Afghanistan aikin tiyatar yi ma ta sabon hanci a nan Amurka


Taliban fighters.

Matar nan ‘yar kasar Afghanistan mai kururrumin hanci, wadda har aka buga hoton ta a bango Mujallar “Time Magazine”, ta iso nan Amurka inda za a yi ma ta aikin tiyatar yi ma ta hanci.

Matar ‘yar shekaru 18 mai suna Aisha, za ta zauna tare da manyan likitocin Los Angeles, a jahar California, su tattauna yadda za a yi ma ta wani sabon hanci, bayan da mugun mijin ta ya yanke ma ta hancin ta da Allah Ya halicce ta da shi. Kunnuwan ta ma a yanke su ke. Aisha, ta ce ‘yan Taliban ne su ka yanke ma ta hancin ta don su yi ma ta horo saboda ta gudu daga gidan mugun mijin ta da azzaluman surukan ta.

‘Yan gwagwarmayar kare mutunci jama’a da ma’aikatan hakkokin bil Adama sun ce sun yi murna, da Aisha za ta samu kulawar likitoci, amma sun yi nunin cewa wasu dubban daruruwan matan kasar Afghanistan su na can su na fama da irin wadannan rigingimun gida.

XS
SM
MD
LG