Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Kwato Makamanmu Daga Hannun Batagari - Rundunar Tsaron Najeriya


Manjo-Janar Abdussalam Abubakar, Kwamandan Rundunar Taro Ta STF
Manjo-Janar Abdussalam Abubakar, Kwamandan Rundunar Taro Ta STF

Rundunar tsaron Najeriya ta 'Operation Safe Haven' ta sha alwashin kwato makamanta da wasu bata-gari da suka kwace a karamar hukumar Bokkos a Jahar Filato.

Kwamandan rundunar Operation Safe Haven da ke aikin samar da tsaro a jihohin Filato da kudancin Kaduna da Bauchi, Manjo-Janar Abdulsalam Abubakar ya ce rundunar ta tamke damarar ganin ta kwato makamanta daga hannun wasu 'yan ta da kayar baya da suka kashe wani jami’in ta guda a wani kauye a karamar hukumar Bokkos ta jhar Filato, suka kuma dauke makaminsa.
A wani taro da yayi da masu ruwa da tsaki da suka hada da sarakunan gargajiya, shugabannin Fulani, da na matasa da mata daga karamar hukumar Bokkos, a Jahar Filato, kwamandan ya ce za su kuma shiga farautar duk wadanda suka boye makaman.
Taron Rundunar Taro Ta STF Da Masu Ruwa Da Tsaki A Jihar Filato
Taron Rundunar Taro Ta STF Da Masu Ruwa Da Tsaki A Jihar Filato

Ya ce ‘’idan ba mu sami kwato makaman ba, babu wanda zai sami sukuni a wannan kauye, saboda za’a iya amfani da makaman wajen kashe mutane da aikata mugayen laifuka kuma ba zamu yadda da hakan ta faru ba.’’

Manjo Janar Abdulsalam Abubakar ya ce akwai wasu mutane 40 da rundunar ke da bayanai a kan su, wadanda kuma ya gargadesu, saboda ya ce ya san abin da suka aikata, da kuma abinda suke shirin yi, domin haka doka za ta yi aikinta a kansu.

Taron Rundunar Taro Ta STF Da Masu Ruwa Da Tsaki A Jihar Filato
Taron Rundunar Taro Ta STF Da Masu Ruwa Da Tsaki A Jihar Filato

Matalolin da mazauna yankin ke fuskanta sun hada da kisan sari-ka-noke, lalata amfanin gona, kisan dabbobi ta hanyar sanya musu guba, barin yara kanana suna kiwo a gonaki, kai hare-hare da ramuwar gayya da sauransu.

Shugaban kungiyar raya al’ummar Butura, a karamar hukumar Bokkos, Philip Julson, ya ce daya daga cikin sinadiran samar da zaman lafiya a yankin shi ne fadawa juna gaskiya kan abin da ke faruwa da kuma tsayuwa kan gaskiyar.

Taron Rundunar Taro Ta STF Da Masu Ruwa Da Tsaki A Jihar Filato
Taron Rundunar Taro Ta STF Da Masu Ruwa Da Tsaki A Jihar Filato

To sai dai a ra'ayin Malam Sale Yusuf Adam, shugaban kungiyar Fulani ta Gan-Allah a karamar hukumar Bokkos, yin adalci ne muhimmin abin da zai samar musu da zaman lafiya a yankin.

A cikin kwankin nan rundunar Operation Safe Haven ta kama bata-gari da dama da suka hada da masu garkuwa da mutane, masu sarrafa makamai da masu kisan ba gaira ba dalili, wadanda rundunar tace dole sai sarakuna da ardo-ardo sun sanya ido kan wadanda ke shigowa yankinsu daga wasu wurare, saboda idan aka sami wani rikici, su ma shugabannin ba za su tsere wa fushin hukuma ba.

Saurari sautin rahoton Zainab Babaji:

Rundunar Tsaro Ta STF Ta Sha Alwashin Sake Kwato Makamanta Daga Hannun Bata Gari
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG