Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Mika Mulki Ga Gwamnatin Farar Hula a Sudan - Burhan


Wani dan aksar Sudan a lokacin yana murnar saukar Ministan tsrao Awad Ibn Auf daga mukaminsa a Khartoun ranar 13 ga watan Afrilu 2019.
Wani dan aksar Sudan a lokacin yana murnar saukar Ministan tsrao Awad Ibn Auf daga mukaminsa a Khartoun ranar 13 ga watan Afrilu 2019.

Daukan wadannan matakai, alamu ne da ke nuni da cewa, zanga zangar da masu rajin kare mulkin Dimokradiyya suka yi, na kara kassara karfin ikon rundunar sojin kasar ta Sudan mai arzikin man fetur.

Sabon jagoran gwamnatin soji ta wucin gadi a Sudan, ya ce, yana da aniyyar mika mulki ga gwamnatin farar hula nan da shekaru biyu masu zuwa, sannan ya ce an soke dokar hana zirga-zirga da aka saka a baya.

Laftanar Janar Abdel-Fatah Burhan, ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa na farko ga ‘yan kasar ta Sudan, wanda aka watsa ta kafar talbijin, inda har ya ba da umurmin a saki dukkanin fursunonin siyasa da aka tsare a zamanin mulkin hambararren shugaba, Omar Al Bashir.

Daukan wadannan matakai, alamu ne da ke nuni da cewa, zanga zangar da masu rajin kare mulkin Dimokradiyya, na kara kassara karfin ikon rundunar sojin kasar ta Sudan mai arzikin man fetur.

Sanarwar na zuwa ne, bayan da shugaban sashen tattara bayanan sirrin kasar, Salah Abdallah Mohammad Saleh, ya yi murabus daga mukaminsa a jiya Asabar.

A kuma ranar Juma’a ne, Ministan tsaron kasar, Manjo-Janar Awad Mohammad Ahmed Ibn Auf, ya sauka daga mukaminsa na shugaban gwamnatin wucin gadi, bayan da ya kwashe kwana guda kacal akan mukamin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG