Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za’a Iya Shawo kan Cutar Shan Inna Kafin Shekara Ta 2018

Wani yaro ana diga mashi maganin rigakafin polio
Wani yaro ana diga mashi maganin rigakafin polio

Kungiyoyin lafiya sunce, zasu iya kauda cutar shan inna kafin shekara ta 2018 idan aka kashe kudi dala biliyan 5.5 da aka kayyade na yin allurar rigakafi da kuma shirin lura da tsaida cutar da kuma sauran kananan cututtukan a duniya.

Masana sunce wannan shiri zai bada kyakkyawar dama na kawar da cutar, wadda ake fama da ita tun 1950, kuma tana gurguntar da mutane da yawa kowacce shekara, amma an kusan kauda ta, ta wurin allurar rigakafi mai inganci da kuma fadakar da jama’a da ake yi.

Ya zuwa 2013, rahotonni da kuma bayanai na nuni da cewa, an sami kananan yara 19 dauke da cutar a kasashe uku - Pakistan, Afghanistan da Nigeria – bayan Indiya tayi bukin cika shekaru biyu da kawar da cutar.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG