WASHINGTON, DC —
Wasu daga cikin wadanda rikicin baya zabe na shekarar 2011, ya shafa a jihar Kaduna, sun yi barazanar kauracewa zabubbukan dake tafe matukar ba’a biyasu diyyar irin hasaran da suka yi ba.
Alhaji Abubakar Sadiq Dahiru, daya daga cikin wadanda suka kira taron manema labarai, a Kaduna, domin nuna wannan damuwar tasu yace jihohi kimanin tara sun amfana da tallafin da Gwamnati tayi alkawari amma har yanzu jihar kaduna shiro.
Daraktan yada labarai na Gwamnan jihar Kaduna Ahmad Abdullahi Maiyaki, yace babu wani abu da zasu cewa wadannan jama’a sai dai hakuri, saboda babu abunda zai iya maye girbin rayukan da aka rasa, ya kara da cewa abun da ya faru mujarrabi ne daga Allah.