Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a yi zabe a kasar Ivory Coast


Wani mutum akan keke, yake wucewa gaban alamar yakin neman zaben jam'iyar Democratic a birnin Abidja kasar Ivory Coast, a zaben da za'a yi Lahadin nan

Lahadi idan Allah ya kaimu za’a yi zaben wakilan Majalisar wakilai a karon farko tun cikin fiye da shekaru goma.

Lahadi idan Allah ya kaimu za’a yi zaben wakilan Majalisar wakilai a karon farko tun cikin fiye da shekaru goma.

Tsohon shugaban kasar Ivory Coastt Laurent Gbagbo
Tsohon shugaban kasar Ivory Coastt Laurent Gbagbo

Ana sa ran cewa jam’iyar shugaba Alassane Ouattara ta Democratic itace zata lashe yawancin kujeru. Haka kuma, kila kiran da magoya bayan tsohon shugaba Laurent Gbagbo suka yi cewa a kauracewa zaben zata taimakawa kawancen Mr Ouattara,

A tarzomar da aka yi kafin zaben na gobe, jami’an kasar sunce mutane uku aka kashe, wasu uku kuma suka ji rauni a ranar Laraba a lokacinda aka aka harba roka a yankin Grand Lahou kafin mohaya bayan shugaba Ouattara suyi wani gangami. Idan ba’a mance ba, an rantsar da shugaba Ouattara bayan da magoya bayansa suka kama tsohon shugaba Gbagbo.

Aika Sharhinka

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG