Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Yi Zaman Durshen Akan Tabarbarewar Tsaro a Kaduna


Matasa
Matasa

Yayin da hare-haren 'yan bindiga sai kara yawa ya keyi da fashewar bamabamai musamman a arewacin Najeriya wasu kungiyoyi sun kuduri yin zaman dushen a garin Kaduna

Hadakar wasu kungiyoyin mata da na matasa sun ce zasu yi zaman durshen har na kwanaki uku a birnin Kaduna kama daga gobe Asabar.

Ibrahim Garba Wala shugaban hadakar kungiyoyin ya yiwa manema labaru karin haske game da dalilin da ya sa suka yanke shawarar yin zaman durshen. Yace zasu zauna, zasu nuna takaici kuma zasu nuna jimami. Kana kuma zasu yi kuka da gwamnati domin irin halin da aka bar arewa.

Mr Wala yace ana ji ana gani ana asarar rayuka. Ana gani ana sake bamabamai ta koina. Ana zuwa makarantu a yanka 'ya'yan mutane kana wasu ana debesu. Duk da wadannan munanan abubuwa wai basu isa a nemi yadda za'a samu masalaha ba. Abubuwan dake faruwa abubuwan takaici ne. Duk safiyar da talaka ya tashi baya jin wani labari mai faranta zuciya. Kullum lamarin sai kara muni ya keyi.

Sabili da abubuwan dake faruwa duk matasan arewa masu kishin arewa da dan Najeriya dake zaune a arewa duk su fito a yi dasu. Kuma duk wani shugaba ko na siyasa ko na sarauta ko wani dai da yace ba za'a yi zaman ba to ba zasu yadda ba. Suna shirye su tona asirin manyan arewa wadanda ake baiwa kudi su yi shuru akan yadda ake tozartawa talaka. Mr Wala yace suna da sunayensu kuma zasu tona asirinsu.

'Yan arewa dake cikin taron kasa da 'yan majalisun arewa dake Abuja duk karya su keyi. An kirasu da babbar murya su watsar da taron kasa da majalisu su dawo arewa. Sai an warware matsalar tsaro kana su koma inda suka fito. Idan babu zaman lafiya a arewa babu wani aiki da zasu yi.

Fatima Garba tace sun shirya domin a yi wanan zaman durshen da su sabili da su ma mata suna cikin wani hali. Matan da suka rasa mazansu daga Yobe, Borno da Adamawa basu da iyaka. Tace ita ma saura kwana hudu a daura mata aure mahara suka kashe saurayinta. Dole ya zama wajibi su fito su tsaya a yi zaman durshen da su domin manyan arewa an rufe masu baki domin abubuwan da suke karba. Sun kira mata kuma babu gudu babu ja da baya.

Ga rahoton Isah Lawal Ikara.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG