Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zabe a Jihar Bauchi


A jihar Bauchi, harkar zaben yau ya gamu da cikas don a yawancin mazabun jihar an sami dan jinkiri wajen kai kayan zabe. A wasu mazabun kuma sun gamu da matsalar rashin aikin na’urar tantance katin zabe.

A wata mazaba da Abdulwahab Mohammed wakilin muryar Amurka ya kai ziyara, jami’in zabe ya fara da bayyana wa jama’a dokoki da ka’idodin kada kuri’a da suka hada da fara tantance mutum don gane wadanda suka cancanta su kada kuri’a.

A cewar wani baturen zabe da Abdulwahab ya gana da shi rashin tsari shi ya kawo masu cikas a mazabar, kuma malaman zaben wurin suyi wa dumbin jama’ar wurin kadan shi yasa shirin bai tafi daidai da yadda aka tsara ba, amma wani kuma ya ci sa'a don yace ba a bata lokaci ba wajen tantance shi.

A jihar Gombe kuma, ya zuwa lokacin da aka hada wannan rahoton, rahotanni na nuna cewa harkar zaben na gudana babu matsala don tun jiya aka kai kayan zabe a mazabu kuma jama’a sun fito domin kada kuri’a.

Sai dai kuma wani bayani da ba a tantance gaskiyarsa ba, na nuna cewa ‘yan boko haram sun bayyana a wasu kauyuka dake karamar hukumar Nafada kuma sun gargadi jama’a kada su je wurin zabe.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG