Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zabe a Maiduguri


Tun da karfe takwas din safiyar yau Asabar daruruwan mutane su ka dinga kwararawa zuwa mazabunsu inda za a tantancesu kuma daga bisani su kada kuri’a.

Wakilin muryar Amurka Haruna Dauda dake maiduguri, ya shaida cewa ya ga mutane a kan layi suna jira a tantance su a lokacin da ya kai ziyara a wasu mazabu, ciki har da wata kwalejin Gwamnati da aka kebe don ‘yan gudun hijira.

A cikin wadanda Haruna Dauda ya zanta da su, wasu sun fada masa cewa har wajen missalin karfe 11 na safiya, lokacin Najeriya, ma’aikatan zaben basu je mazabar ba amma jama’ar wurin sun ce za su jira har sai ma’aikatan sun zo.

Wakilin na muryar Amurka ya kuma gana da daya daga cikin malaman zabe a garin Gwoza kuma ya shaida masa cewa komai na tafiya daidai a mazabar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:53 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG