Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015:INEC Ta Gargadi Masu Katunan Bogi

Yaponiya - Miss İnternational 2016

Yaponiya - Miss İnternational 2016

Nick Dazan, mukadashin direktan hulda da jama'a na hukumar zaben Nigeria, yace duk wanda yaje yin zabe da katin jabu, yayi aikin banza.

Da zarar mutum yaje zabe, kuma katin sa ne wanda hukumar zabe ta bashi. Na'urar tantance kati zata baiyana suna da dukkan bayanan da aka dauka a lokacinda mutum yayi rajista.

Nick Dazan, mukadashin direktan hulda da jama'a na hukumar zaben Nigeria shi yayi wannan bayani a hira da Sahabo Imam Aliyu yayi dashi.

Mr. Dazan yace duk wanda yaje da katin jabu domin yin zabe, to yayi aikin banza, domin katin ba zai nuna dukkan bayana da aka dauka ba, kamar addreshi da lambar waya da sauran bayanin da mutum ya bayar a lokacinda aka yi masa rajista.

Yace za'a yi tantancewar ne a gaban yan jarida da masu lura da zabe da wakilan jam'iyun siyasa da kuma dukkan wadanda ya kamata, a saboda ayi adalci.

A saboda haka masu saye da sayar da katuna zaben su, sunyi aikin banza domin a gare su kwaliya ba zata biya kudin sabulu ba.

ZABEN2015: Hukumar Zaben Nigeria, Tace Duk Wanda Yaje Zzabe da Katin Jabu, Domin Yayi Zabe, Yayi Aikin Banza - 4'15"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:15 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG