Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2019: MAGOYA BAYAN ATIKU SUN ZABURO


Atiku Abubakar da Shugaba Muhammadu Buhari
Atiku Abubakar da Shugaba Muhammadu Buhari

A Najeriya wasu har sun fara kada gangar siyasar 2019, yayin da wasu ke ganin lokaci bai yi ba tukunna.

Tun daga yanzu wasu magoya bayan tsohon Shugaban Najeriya kuma jigo a jam'iyyar APC, Atiku Abubakar (Turakin Adamawa) sun fara tuna ma 'yan Najeriya cewa za su so gwaninsu ya yi takara a shekara ta 2019.

An mai da bukin kaddamar da wata hanya a jahar Adamawa wata dama ta rada ma 'yan Najeriya cewa Turaki fa na nan tafe a 2016. Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Jahar Adamawa Alhaji Abdurrahman Abba Jimeta, ya ce lokaci ya wuce da mai kaza zai ci kai. Ya kara da cewa naka sai naka, Don haka su 'yan Adamawa za su taka rawar gida.

Alhaji Abdurrahman ya kara da cewa idan ba don Turakin na Adamawa ba, da ba a yi siyasar da ta gabata ba. Ga masu gain Turaki ba zai kai labari ba, sai Abdurrahman ya ce daga zaben Trump na Amurka sun gane cewa Allah ne ki ba da mulki saboda kafin zaben an dauk sam Trump ba zai kai labari ba.

Ga wakilinmu na Adamawa Ibrahim Abdul'aziz da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

XS
SM
MD
LG