Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Shugaban Kasar Burkina Faso


Wani dan kasar Burkina Faso yana kada kuri'arsa, lahadi 21 Nuwamba 2010 a Ouagadougou, babban birnin kasar.
Wani dan kasar Burkina Faso yana kada kuri'arsa, lahadi 21 Nuwamba 2010 a Ouagadougou, babban birnin kasar.

Ran lahadi ce ake gudanar dazaben shugaban kasar Burkina faso dake Afirka ta yamma. Zaben da ake kyautata cewar zai sake maida shugaba Mai ci a yanzu, Blaise Compaore kan kujerar shugaba kasa a karo na hudu.

Rahotanni na cewa zaben shugaban kasar Burkina Faso a ran lahadi babu wasu fitattun ‘yan hamayyar dake kalubalantar shugaba Blaise Compaore, wanada ake kyautata cewar shine zai sake samun nasaraakaro na hudu da zai ci gaba da shugabancin kasar Burkina faso.

Mr. Campaore, a shekarar 1987 ce ya kwaci mulki a wani juyin mulkin sojan dayayi jagoranci.Wanda ke takarar tare da Mr.Campaore shine Lauya Benewende Sankara, kuma aqna kyautata cewar wadanda suka cancanci kada kuri’a kusanmiliyan uku da dubu dari biyu zasu je rumfunan zaben na ranar lahadi.

A farkon wannan shekarar ce jam’iyyar da Mr. Campaore ke yiwa jagoranci ta “Congress for Democracy” tace tana da niyyar tabbatar da soke wa’adin shekaru ga duk shugaban kasar da za’azaba a kasar Burkina faso.

XS
SM
MD
LG