Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Shugaban Kasar Ghana Na Ranar Disamba 07, 2016

Jiya Laraba bakwai ga watan nan al'ummar Ghana suka gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu

Bisa ga rahotanni da aka samu zabukan sun gudana cikin kwanciyar hankali da lumana.

'Yan takara bakwai ne suka tsaya neman shugabancin kasar amma biyu ne suka fi fice. Akwai shugaban kasa mai ci yanzu John Dramani Mahama na jam'iyyar NDC da madugun 'yan adawa Barrister Nana Akufo Addo na jam'iyyar NPP.

Za'a samu cikakken sakamakon zaben ranar Asabar mai zuwa kodayake daga gobe ana iya soma samun sakamako daga sassan kasar daban daban

Domin Kari

XS
SM
MD
LG