Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 'Yan Majalisu a Britaniya


Daya daga cikin bangarorin ginin majalisar dokokin Britaniya
Daya daga cikin bangarorin ginin majalisar dokokin Britaniya

Masu kada kuri’a a kasar Britaniya sun nufi rumfunan zabe yau Alhamis don yin zaben ‘yan majalisa, abinda ra’ayoyin jama’a ke nuna cewa yanzu haka ba za a iya hasashen sakamakon zaben ba.

Sakamakon ra’ayoyin jama’a a jiya Laraba ya nuna cewa jam’iyyar masu ra’ayin rikau ta Firai minista David Cameron ta sami goyon baya da kashi 33 daga cikin dari na masu kada kuri’ar Britaniya.

Ita kuma babbar jam’iyyar adawa ta Ed Milliband na bayanta da maki daya.

Ra’ayoyin na jama’a sun nuna cewa sakamakon zaben ka iya tilasta daya daga cikin manyan jam’iyyun kasar guda biyu kafa gwamnatin kawance da wata daga cikin sauran jam’iyyun da basu da kujeru da yawa a majalisar mai kujeru 650.

Masu nazari sun ce wannan zaben na Britaniya shine mafi wuyar hasashe da aka taba gani kuma yana da muhimmanci.

XS
SM
MD
LG