Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zafi Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutane 6 A Amurka


Hukumomin Amurka sun dakatar da sauka ko tashin jiragen sama saboda tsananin yanayi zafi a birnin Phoenix,

Har yanzu ana ci gaba da fama da wani mummunan zafin da ya riga yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 6 a yankin kudu maso yammacin Amurka.

A yayin da tsananin zafin ya ragu kadan jiya jumma’a a Los Angeles, mazauna birnin suna kara damarar fuskantar zafi mai tsanani a wannan lokaci na zafi a Amurka.

A farkon makon nan, sai da aka dakatar da sauka ko tashin jiragen sama a birnin Phoenix a lokacin da zafi ya cira sama zuwa digiri 45 har ma fiye da haka a wasu sassan kudu maso yammacin Amurka, kama daga birnin Tucson a Jihar Arizona har zuwa Palm Springs a Jihar California.

Mutane sun yi bakin kokarinsu na kaucewa zafin ta hanyar hallara a manyan dakunan taron da aka sanya musu na’urorin AC a garuruwa da birane da kauyukan yankin.

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG