Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zamu Rufe Sansanan 'Yan Gudun Hijira 29 Ga Mayu-Kashim Shetimma


Mata Da Yara A Sansanin 'Yan Gudun Hijira Na Fufore
Mata Da Yara A Sansanin 'Yan Gudun Hijira Na Fufore

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya sake jadada aniyarsa ta takawa kungiyoyi dake samar da agajin gaggawa birki bisa yadda yace suna amfani da ‘yan gudun hijira a jihar wajen azurta kansu maimakon agazawa mutanen dake bukatar wannan taimakon.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar kasafin kudin bana daga majalisar dokokin jihar Borno, da kakakin majalisar Abdulkarim Lawan y ya kima masa a fadar gwamnatin jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa, bai gamsu da kokarin da yace kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya suke yi ba, domin bisa ga cewarshi, yawan kudin tallafin da suke badawa yana tafiya ne a kansu, ya bada misali da cewa, zaka ga sun gina bandaki biyar a garin Goza amma su tashi a jirgi mai saukar angulu sau bakwai.

Gwamna Shatimma yace bisa wannan dalilin zasu rufe dukan sansanan ‘yan gudun hijira a jihar ranar ashirin da tara ga watan Mayu mai zuwa, domin mutane su koma gidajensu su ci gaba da rayuwa cikin mutumci.

Gwamnan ya bayyana matsalolin dake addabar jihar a matsayin “matatsa” da kowa ke zuwa da sunan taimako amma basu gani a kasa. Yace akwai wadanda ke zuwa jihar su kama gidajen haya na tsawon shekaru kamar suna fatar matsalolin su ci gaba.

Ga cikakken rahoton da wakilinmu a jihar Borno Haruna Dauda Bi’u ya aiko mana.

Rahoton kungiyoyin sa kai a jihar Borno:3:40"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG