Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-zanga: Birnin Paris Na Ci Da Wuta!


Wata wutar da masu zanga-zanga su ka tayar

Duk da janye shirin kara farashin man fetur da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi, har yanzu masu zanga-zanga a birnin Paris na cigaba da banga ma kaddarori wuta.

'Yan sanda a Faransa sun jefa barkonon tsohuwa kan masu zanga-zanga a shahararren dandalin nan na Champs - Elesees. Masu zanga-zangar na nuna damuwarsu ne kan tsadar rayuwa a Faransar.

'Yan sanda sun ce masu zanga-zanga akalla 1,500 ne su ka bazu kan titunan birnin Paris, kuma an kama a kalla 127 daga cikinsu.

A shirinta na tinkarar mako na hudu na wannan zanga-zangar, kasar ta Faransa ta rufe hasumiyar Eiffel da kuma wasu sanannun wuraren yawon bude ido, sannan ta sa dubban jami'an tsaro cikin shirin ko-ta-kwana.

An rufe shaguna da dama a birnin na Paris kafin zanga-zangar ta yau Asabar don kauce ma fushin masu zanga-zangar da kuma wasoso.

Tun da aka fara zanga-zangar a watan jiya saboda tsadar man fetur, mutane hudu sun mutu a wasu al'amura masu nasaba da zanga-zangar.

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG