Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zargi Cin Zarafin Saduwa Ga Dakarun Majalisar Dinkin Duniya Ya Karu


Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon
Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon

Zargin tursasa saduwar jima’i akan rundunar kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ta karu sosai a shekarar 2015 data gabata, duk kuwa da tsananin dokar ba sani ba sabon hukumar ga duk wanda aka kama da wannan laifi.

Kamar yadda wani rahoto da ya fito daga ofishin Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya nuna a ranar Juma’a, ya nuna cewa, an sami rototon cin zarafin na saduwa har guda 99 inda ya wuce na shekarar 2014 da aka sami rahoton 80.

Yawancin zarge-zargen sun fito ne daga ko dai inda sojojin da ‘yan sandan kiyaye zaman lafiyar na MDD suka gama aiki ko kuma wajen da suke kan aikin kawo zaman lafiyar.

Wani karamin Sakataren ayyukan majalisar Atul Khare yace, ba zamu yarda da irin wannan aika-aikar ba, ta kyale wadanda ya kamata su kare al’umma kuma su zama sune dodanninsu ba.

XS
SM
MD
LG