Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZAUREN MATASA: Damina Ta Kankama Amma 'Yan Bindiga Sun Hana Shiga Gonakin Da Ke Nesa Da Gari, Kashi Na 8 - Satumba 25, 2023


Nasiru Adamu
Nasiru Adamu

Ci gaba da Zauren Matasa a garin Dan Umaru mai yawan jama'a da matasa manoma da ke karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi arewa maso yammacin Najeriya.

Matasa sun taru a zauren inda su ka koka da cewa ga dai damuna ta kankama amma miyagun iri sun hana shiga gonaki da ke nesa da gari. Matasan na bukatar dauki daga hukumomi don kar hakan ya zama barazana ga samarda abinci yayin da janye tallafin fetur ya jefa talakawa cikin kuncin rayuwa.
Ra'ayin matasa na nuna ko dai ba za a samu yin noman yanda a ka saba ba; to mutane su samu yin barci da ido biyu rufe.

A makon jiya mun fara duba hanyoyin motsi ya fi labewa wajen kare kai daga tarkon miyagun iri maimakon zama a sunkuru don tsananin fargaba.

Saurari shirin:

ZAUREN MATASA
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:09:40 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG