Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zazzabi: An Gargadi ‘Yan Nijar Su Yi Taka Tsantsan Da Zuwa Sakkwato.


Sauro na yada wata shu'umar cutar zazzabi

Yayin da wani shu'umin zazzabi ke barazana ga harkokin yau da kullum a jahar Sakkwaton Najeriya, Janhuriyar Nijar mai makwabtaka ta Najeriyar, ta shiga daura damara.

Jami’an asibiti a Janhuriyar Nijar da ke makwabtaka da Najeriya sun yi gargadi ga ‘yan Nijar da su yi kaffa-kaffa da zuwa jahar Sakkwato ta Najeriya ganin yadda wani shu’umin zabbin cizon sauro mai kisa ya yadu a wasu sassan jahar.

Jami’an asibiti a birnin Konni da ke kusa da Najeriya sun shiga yin gargadi ga ‘yan kasuwar Janhuriyar Nijar da kuma masu kai ziyarce-ziyarce tsakanin makwabtan kasashen da su yi hankali kar su yada cutar ko kuma su kamu da ita. Jami’in Hulda da Jama’a na Asibitin Birnin Konni, Malam Hassan, ya gaya ma wakilinmu na shiyyar Konni Haruna Mamman cewa sun shiga wannan gargadin ne duk kuwa da cewa wannan cutar ba ta iso Janhuriyar Nijar ba. To amma ya yi kira ga duk wanda ya ji alamar zazzabi ya garzaya asibiti don a tantance.

Hukumar Asibitin Birnin Konni ta ce za ta so ganawa da takwararta ta jahar Sakkwaton Najeriya don tattauna yadda za a taimaka ma juna, muddun ta samu izini daga Ma’aikatyar Lafiya ta Janhuriyar Nijar.

Ga wakilinmu Haruna Mamman da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

XS
SM
MD
LG