Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zazzabin Cizon Sauro Ya Kashe Dalibai a Jihar Kebbi


Wadansu dalibai

Jami’an lafiya daga ma’aikatar lafiya na jihar Kebbi suna binciken mutuwar dalibai guda uku na makarantar sakandire ta Kanta a karamar hukumar Argungu, ta jihar Kebbi.

Jami’an lafiya daga ma’aikatar lafiya na jihar Kebbi suna binciken mutuwar dalibai guda uku na makarantar sakandire ta Kanta a karamar hukumar Argungu, ta jihar Kebbi.

An baiyyana cewa daliban sun mutu sakamakon wata cuta mai kama da zazzabin cizon sauro.

Kwamishinan ilimi na jihar, Abdulmumin Samaila Kamba, yace kungiyar masanan lafiya daga ma’aikatar lafiyar sun tafi makarantar domin su yi bincike.

"Dalibai uku sun rasa rayukan su, daya daga jihar katsina da kuma biyu daga jihar Kebbi. Ya zuwa yanzu, bamu san dalilin mutuwarsu ba, sai jami’an kiwon lafiya daga ma’aikatar lafiya sun da kuma likitocin kasa da kasa sun tabbatar cewa zazzabin cizon sauro ne ya kashe su.”

Har yanzu suna ci gaba da yin gwaje gwaje a makarantar kuma sauran daliban da suka kamu da cutar suna samun sauki” in je kwamishinan. Shugaban makarantar, Bala Yaldu, yaki yayi magana kan yanayin.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG