Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zazzabin Lasa Ya Kashe Mutane 16 a Jahar Naija


A yi hankali da bera
A yi hankali da bera

Ga dukkan alamu zazzabin lasa na cigaba da lakume rayuka a sassan Najeriya. Wannan kuma bai rasa nasaba da rashin fadakar da jama'a game da illar nau'in berayen da ke yada zazzabin

Zazzabin Lasa, wanda wani nau’in bera ke yadawa, na cigaba da haddasa mace-mace a sassan Najeriya. Na baya-bayan nan shi ne kashe mutane a kalla 16 da wani zazzabin da ake kyautata zaton na Lasa din ne ya yi a jahar Naija.

Ma’aikatar Lafiyar Jahar Naija, wadda ta tabbatar da mutuwar mutane 16 din, ta shiga fadakar da mutane game da illar cutar. Ta ce ta aike da samfurin cutar dakunan bincike don tabbatar ko ita ce ko kuma wata mai kama da ita ce.

Kwamishinan Lafiya na jahar Naija, Dokta Mustapha Jibrin ya shawarci mutane su tabbata beraye ba su fitsari ko kashi kan abincinsu ko kuma duk wani abubuwan da su ke mu’amala da su. Ya bayyana alamomin kamuwa da cutar ta Lasa.

Ga dai wakilinmu Mustapha Nasiru Batsari da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG