Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Kwamitin Majalisar Dattawa dake Sa Ido A Harkokin IDPs A Arewa Maso Gabashin Najeriya

Kwamitin Majalisar Dattawan a karkashin jagorancin Sanata Shehu Sani ya ziyarci sansanin 'yan gudun hijira a jihohin Adamawa da Borno

Ziyarar da kwamitin ya kai ya gano cewa kudaden da gwamnatin tarayya ta bayar fiye da nera biliyan 8 domin a taimakawa masu gudun hijira tamkar wawuresu aka yi saboda wadanda ya kamata su ci gajiyar kudin basu ci ba.

Inji Sanata Shehu Sani yace wasu tsiraru dake zaune a Abuja suke amshe kudin amma basu taba zuwa jihohin da rikicin Boko Haram ya daidaita ba balantana ma su san halin da 'yan gudun hijira ke ciki, mutanen da suka yi hasarar muhallansu, mata sun rasa mazajensu kana yara sun zama marayun dole.

Baicin haka 'yan gudun hijiran ba sa samun abinci isasshe, babu tufafi, wurin kwanciyarsu kuma tamkar na awaki ne. Yara basa zuwa makaranta , makarantaun dake akwai Majalisar Dinkin Duniya ce ta samar dasu. Asibitocin da suke anfani dasu sojoji ne suka kafa su. Dan abincin da suke samu wasu bayain Allah ne suke taimakawa.

Shehu Sani yayi alkawarin binciken lamarin da zara sun koma Abuja tare da bada tabbacin za'a hukumta duk wadanda aka samu da hannu a wawure kudin bayin Allah.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG