Dokar-Ta-Baci Ta Hana Jihohi Uku Cin Moriyar Shirin Samun Taki

Amma kuma karamin ministan ayyukan gona Bukar Tijjani yace za a yi amfani da kundin manoma na bara domin sayar musu da taki a bana
Karamin ministan ayyukan gona na Najeriya, Bukar Tijjani, yace tsinke layukan wayoyin salula da aka yi a sanadin dokar-ta-baci a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe, ya sa ba za a yi amfani da shirin sayarwa da manoma takin zamani ta hanyar amfani da wayoyin salula a bana ba.

Ministan, wanda yake magana a garin Gombe, yace wadanda suka kai taki zuwa wadannan jihohi uku a shekarar da ta shige, sun yarda cewa za su yi amfani da kundin manoman da suka yi rajista domin wannan shiri a bara, domin sayarwa da manoman taki a bana.

Da yake magana kan tsoron da ake yi na fuskantar karancin abinci a saboda rashin tsaro a wadannan jihohin, ministan yace, karancin ba zai yi tsanani ba, ko da ma an yi. Yace shugaba Goodluck Jonathan ya bayarda umurnin da a kai agajin abinci na motoci akalla 600 domin agazawa mutanen da rikicin ya shafa.

yace wasu attajirai ma kamar Alhaji Aliko dangote, sun yarda zasu tallafa wajen kai kayan agajin abincin.

Ga cikakken bayanin ministan na aikin gona.

Your browser doesn’t support HTML5

Dokar-Ta-Baci Ta Sa Za Ayi Rabon Taki Ban Da Jihohi Uku - 2:59