Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sultan Sa'ad Abubakar Yace Ba 'Yan Najeriya Na Ainiihi ke Haddasa Tashe-Tashen Hankula Ba


Sultan Muhammadu Saad Abubakar III, Sarkin Musulmin Najeriya

Sultan din yace wasu daga kasashen waje ne suke kokarin ruguza Najeriya, kuma za a ga bayansu a saboda addu'o'in da aka sanya a gaba

Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar, yace ba 'yan Najeriya na asali ne suke haddasa tashe-tashen hankualn da suke faruwa a kasar ba.

Yace 'yan Najeriya su na kaunar junansu ta yadda ba zasu iya irin wadannan kashe-kashen na junansu ba. Yace wasu ne kawai daga kasashen waje suka zo su na kokarin ruguza Najeriya.

Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar, yana magana ne a wurin bukin ranar kabilar Nupe ta wannan shekarar da aka gudanar a garin Bida a Jihar Neja.

Yace dukkan abubuwan da suke faruwa a yankin arewa maso gabas, da wasu sassan Najeriya, ba aikin asalin 'yan Najeriya ba ne, kuma da ikon Allah za a ga bayan wadannan.

A wurin wannan bukin ne kuma, gwamna Babangida Aliyu na Jihar Neja, ya fito karara yace gwamna Rotimi Amaechi na Jihar Rivers, shi ne halaltaccen shugaban kungiyar gwamnoni ta Najeriya, domin a fili aka gudanar da zabe ya samu kuri'u 19, yayin da gwamna Jonah Jang na Jihar Filato wanda ke ikirarin cewa shi ne mai wannan mukami, ya samu kuri'u 16.

Ga cikakken rahoton da Mustapha Nasiru Batsari ya aiko.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:14 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG