Shugaba Good Luck da Siyasar Adamawa

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Dambarwar siyasar jihar Adamawa bazata rasa nasaba da takardan da Gwamnan jihar Murtala Nyako, ya rubuta ba na zargin shugaba Good Luck Jonathan, dangane da tashen hankalin da ya addabi yankin arewa maso gabas.

Farfesa, Kabiru Mato, na Jami’ar Abuja , ne ya bayana hakan a lokaci da suka tattauna da wakilinmu ta wayan tarho.

Ya kuma kara da cewa fitar Murtala Nyako, jamiyar PDP, shima wani abun ne da ya ci gaba da tayarmasu da hankali, ganin yanda jamiyar ke kokarin zawarcin wadanda suka canja sheka daga jamiyar.

Farfesa Mato, yace Murtala Nyako.kwararre ne ta fuskokin da dama, yace ko a cikin kungiyarsu ta APC kai tsaye yake fadin gaskiyarsa ta yanda ya fahimceta wanda kuma so dayawa baya masu dadi.

Your browser doesn’t support HTML5

Siyasar jihar Adamawa - 3'43"