WASHINGTON, DC —
An samu kimanin mata talatin da suka samu kubuta daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram daga dajin Sambisa.
Matan, wadanda yanzu haka suke Madagali, ta jihar Adamawa, sun ce sunyi tafiya ta fiye da kilomita goma kafin su isa garin na Madagali dake makwabtaka da jihar Borno, inda ake tallafa masu.
Da yake tabbatar da labarin shugaban karamar hukumar Madagali, Mr. James Watarda, yace mata talatin da yara ne suka tsira zuwa garin na Madagali inda karamar hukumar ke tallafa masu.
Yace duk kansu an kaisu asibiti domin a duba lafiyar jikinsu dana ‘yayan su, ya kara da cewa yakamata gwamnatin ta gaggauta taimaka masu.
Matan sun ce sun tsira ne bayan da suka haura Katangar da aka gina aka kewaye inda suke tsare ciki a dajin na Sambisa.