Shugabar kungiyar agajin likitoci ta MSF ta ce annobar cutar Ebola da ake fama da ita, tana matakai dabam-dabam a kasashe uku.
Dr. Joanne Liu ta fada cewa lamarin ya fara daidaita a kasar Guinea, a yayin da cutar ke kara bazuwa gadan-gadan a kasashen Saliyo da Liberiya.
Dr. Liu ta ce ba kamar barkewar annobar wannan cuta ta tsawon kimanin makonni 8 kawai da aka gani a baya ba, a wannan karon zai dauki watanni kafin a shawo kanta. Ta ce wani bambancin kuma a wannan karon shi ne cutar tana shiga manyan garuruwa da birane maimakon a kauyuka kalilan kamar yadda aka gani a baya.
Hukumar kiwon lafiya ta MDD ta ce mutane 1,145 ne suka mutu ya zuwa yanzu daga wannan cuta ta Ebola a Afirka ta Yamma.
Your browser doesn’t support HTML5
Za A Shafe Watanni kafin A Shawo Kan Ebola - 0'55"