Ma'aikatar kiwon lafiya ta Najeriya ta ce ta tabbatar da cewa an samu wata karin mace guda da ta kamu da cutar Ebola a Lagos, yayin da jami'an Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya suka gana domin tattauna da'a ko rashinta, ta yin amfani da magani na gwaji wajen takalar wannan annoba da ta barke.
Jami'ai a Najeriya sun ce daya daga cikin ma'aikatan nas da ta kula da wani dan Liberiya da ya mutu da cutar a Lagos, ita ma ta kamu da wannan cuta, abinda ya kawo adadin wadanda aka tabbatar su na dauke da wannan cuta a Najeriya zuwa 10, dukkansu a Lagos. Biyu daga cikinsu sun mutu.
Najeriya, Liberiya, Guinea da kuma Saliyo su na gwagwarmayar shawo kan wannan cuta wadda a yanzu ta kashe mutane kusan dubu daya.
Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta ayyana wannan annoba a zaman matsalar gaggawa ta rashin lafiya a duniya. Jami'an bangaren da'a na hukumar sun gana yau litinin a Geneva domin tattauna yiwuwar amfani da magunguna na gwaji wajen shawo kan annobar.