Tsohon shugaban soja na Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Banagida mai ritaya, ya roki hukumomi da su gudanar da bincike sosai kan salsalar amfani da mata da ake yi a zaman 'yan kai harin kunar bakin wake, yana mai cewa yin hakan zai kai ga samo hanyar ja ma lamarin burki.
Da yake magana da 'yan jarida a lokacin taron addu'ar da aka kira na cikarsa shekaru 73 da haihuwa, Janar Babangida yace shi ba ya tsammanin cewa dalibai mata na makarantar sakandaren Chibok wanda 'yan Boko Haram suka sace ne ake amfani da su a kai hare-haren ba.
Ya roki jama'a da su bayarda cikakken hadin kai ga gwamnati domin a kawo karshen wannan sha'anin rashin tsaron da ake fama da shi.
Da yake kare sojojin Najeriya dake shan sukar cewa sun kasa kawo karshen wannan lamarin, Janar Babangida yace ba zai yiwu a kawo karshen wannan abin cikin kwana guda ko mako guda ba, yana mai misali da yakin basasar Najeriya wanda tun farko aka ce za amagance shi cikin kwana guda, amma sai da aka shafe shekaru uku ana yi.
Yace ba ya fata, kuma ba ya tsammanin cewa za a shafe shekaru uku nan gaba ana fama da wannan matsala ta rashin tsaro a arewa maso gabashin Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5
Janar Babangida Yace A Binciki Yadda Ake Amfani Da Mata Wajen Kunar Bakin Wake - 2'59"