Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Chadi Sun Kwato Wasu Yaran Da 'Yan Boko Haram Suka Sace

Sojojin Chadi
Sojojin Chadi

Jami'ai sun bayyana cewa dakarun kasar Chadi sun ceto wasu 'yan Najeriya wadanda 'yan kungiyar Boko Haram suka sace kwanakin baya.

Tsageran na Boko Haram sun sace wadannan yara ne ranar lahadin da ta shige a wani farmakin da suka kai kan garin Doron Baga dake kusa da bakin iyaka da Chadi.

Sojojin Chadi sun tare 'yan bindigar tare da wadannan yara su kusan 100 da suka sace a bakin iyaka.

Ba a san ko yaya sojojin na Chadi suka yi da 'yan bindigar na Boko Haram ba, ko kuma sun mayar da wadannan yara da aka sace zuwa gida.

Ana zargin kungiyar Boko Haram da sace daruruwan mutane a yankin arewa maso gabashin Najeriya domin amfani da su a zaman sojojin tilas, ko matan aure ko kuma masu musu aikin boyi-boyi.

Sace dalibai mata masu yawan gaske da Boko haram ta yi a ranar 14 ga watan Afrilu daga garin Chibok, ya janyo hankalin duniya sosai ga wannan rikicin tare da tayin agaji daga kasashen yammaci.

XS
SM
MD
LG