WASHINGTON, DC —
Wani na hannun damar Nuhu Ribadu, yace tsohon dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar ACN a Najeriya, kuma jigo a babbar jam'iyyar adawa ta APC, ya yi rajista a jam'iyyar PDP.
Alhaji Isa Ibrahim Toungo yace Ribadu yayi rajista a gundumarsa ta Bako dake karamar hukumar Yola ta Kudu kuma har an ba shi katin jam'iyyar PDP mai lamba 1933795.
Yace ana sa ran cewa nan da ranar litinin shi da kansa Nuhu Ribadu zai fito ya ayyana komawa jam'iyyar PDP inda ake jin cewa zai yi takarar gwamnan Jihar Adamawa karkashin laimarta.
Ga cikakken bayanin da Alhaji Toungo yayi mana kan komawar Nuhu Ribadu cikin PDP