Sakataren Harkokin Wajen Amurka Zai Gana da Wasu Ma'aikatansa Akan Siriya

John Kerry, Sakataren Harkokin Wajen Amurkay

Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya ce ya na shirin ganawa da wasu ma'aikatan Ma'aikatarsa

. Ma'aikatan sun mika wata bukatar neman Amurka ta kara kaimi a Siriya da zummar kawo karshen rikicin kasar, amma ba'a sani ba ko Kerry ya amince da bukatar tasu ba.

Da 'yan jarida su ka tambaye shi jiya Litini ko ya karanta bukatar ma'aikatan, Kerry ya ce ya karanta, sannan ya kara da cewa, "Al'amari ne mai kyau."

Ya ce zai gana da wasu daga cikin manyan jami'an diflomasiyya 51 din, wadanda su ka yi kiran da Amurka ta fahimci muradun gwamnatin Siriya sosai bisa ga a hare-haren jiragen sama da take kaiwa da taimakon Rasha.

Bukatar jami'an diflomasiyyar, wadda aka mika ta wata kafa ta ma'aikatar, ta fito fili ne a makon jiya bayan da aka tseguntawa wasu kafafen yada labarai da dama

Wani mai magana da yawun Ma'aikatar John Kirby, ya ce Kerry ya yi imanin cewa jami'an diflomasiyyar sun gabatar da bukata mai ma'ana. Saidai bai ce Kerry na goyon bayansu ba.