Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tace Barazanar Ta'adanci A Duniya Na Kara Bazuwa


 John Kerry sakataren Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka
John Kerry sakataren Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka

Barazanar ta'adanci a duniya tana kara bazuwa, inda kungiyoyi kamar ISIS, take yada jijiyoyinta a sassa da suka hada da kudu maso gabashin Asiya, da wasu sassan Rasha, da kuma Afirka, kamar yadda rahoton Ma'aiatar harkokin wajen Amurka na shekara shekara ya bayyana.

Rahoton yaci gaba da cewa, yayinda kungiyoyi kamar al-Qaida, da Boko Haram da al-Shabab suke ci gaba da kai hare hare da nufin gurgunta harkokin kasashensu, ISIS ta ci gaba da zama babbar barazana a duk fadin duniya a bara, inda take da "dakaru masu yawa da karfi" a Syria da kuma Iraqi.

Rahoton ya ci gaba da cewa, koda shike karfin mayakan kungiyar ya ragu a wani lokaci a bara, duk da haka 'yan yakin sakan kungiyar sun lallaba suka kai jerin hare-hare a wasu wurare da suka hada da Faransa da kuma Turkiya.

Haka nan rahoton na Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurkan ya ci gaba da cewa, ISIS ta yi karfi a Libya, kuma ta kafa rassa a a Afghsnisdtan, da Pakistan da kuma Najeriya.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurkan tana ayyana kungiyoyi daban daban har 60 a zaman kungiyoyin 'yan ta'adda a rahoton nata na shekara shekara, haka nan tana ambaton kasashe da take kallonsu a zaman wadanda suke hana ruwa gudu a fafaftawa da ake yi da ta'addanci.

XS
SM
MD
LG