Hukumomin Tanzaniya Sun Nemi a Sako Mutane 21 a "yan Tawayen Congo Suka kama

Mayakan Mai-Mai Feb. 4, 2009.

A jiya laraba ne Mahukunta a kasar Tanzania, suka roki shugabannin kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo su taimaka a sakar musu ‘Yan kasar su har su 21 da suke tsare dasu tun watan jiya wadanda yan tawayen Mai-Mai na jamhuriyar Africa ta Tsakiya suka kame

‘Yan tawayen Mai-Mai sun kame mutanen ne tun a ranar 28 ga watan jiya a wurin da ake kira Lulimba, dake kudancin lardin Kivu, lokacinda suke akan hanyar su ta zuwa inda ake hakar zinari a gundumar Maniema, inji maimagana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Kasiga.

Su dai sojojin kasar ta Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo suna yakar ‘yan kungiyar ta Mai-Mai ne dake kudancin Kivu, Sojojin na Congo suka ce tuni mutane 12 suka mutu sakamakon arangamar da akayi da wadannan mayakan.

Wannan dai ba shine karo na farko da direbobin kasar ta Tanzania suka fada hannun ‘yan Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo ba.

Domin ko a cikin watan satunba, sai da yan tawayen na Mai-Mai suka kona motocin Tanzaniyan guda 4 kana suka kame direbobi 8 a kudancin Kivu.