Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Hallaka Jami'an Majalisar Dinkin Duniya A Demokaradiyyar Kongo


An samu gawarwakin jami'an bincike na majalisar dinkin duniya da mai masu tafinta a Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo (DRC).

Mai magana da yawun gwamnatin ta DRC, Lambert Mende ya fadi jiya Talata cewa an sami gawarwakin na Micheal Sharp da Zaida Catalan da Betu Tshintela ne a wani wurin da ke daura da kogin Moyo, a lardin Kasai da ke yankin tsakiya.

Da ya ke magana da Sashin Faransancin Afirka na Muryar Amurka, Mende ya ce an ma fille kan Catalan.

Majalisar dinkin duniya ta tura Mr. Sharp, ba-Amurke da Mr. Catalan, dan kasar Sweden, ne don su binciki zargin cin zarafin bil'adama wanda aka aikata a kusa da kauyen Bunkonde, wanda ke kudu da hedikwatar lardin Kananga.

Sun bace ne ran 12 ga watan Maris tare da mai masu tafinta Tshintela, dan asalin kasar Congo, da kuma wasu 'yan asalin kasar ta Congo, su uku, da direbansu Isaac Kabuayi, da wasu masu babura biyu da ba a tantance su ba.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG