An Cimma Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Sudan Ta Kudu

Shugaban 'Yan Tawaye Riek Machar

A jiya Laraba ne kungiyoyin da suke gaba da juna a Sudan ta kudu, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da suka kira ta karshe da zata kawo karshen yakin basasar kasar na tsawon shekaru biyar.Fadan da ya halaka dubun dubatan jama'a ya kuma tilastawa miliyoyi barin muhallansu.

Sassan biyu sun sanya hanu kan wasu yarjejeniyoyi na wucin gadi,amma duka bangarorin sun fada cewa wannan ce ta karshe.

Shugaba Salva Kiir, da shugaban 'yan tawaye Riek Machar, dama shugabannin wasu kungiyoyin hamayya, duk sun sanya hanu kan yarjejeniya ta "karshe" a makwabciyar kasa Ethiopia, kamar yadda kakakin gwamnatin ta Habasha, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press.