Saudiyya Ta Canza Tsarin Shiga Wuraren Cin Abincin Kasar

Saudi Arabia

Rahotanni na nuna cewa kasar Saudi Arabiya za ta soke tsarin nan na banbanta kofofin mata da kofofin maza a wuraren cin abinci.

Masu shagunan sayar da abinci a kasar sun dade suna neman mabiya addini, da shugabannin kasar, da su soke wannan dokar, domin samun saukin yin mashiga guda daya ta kowa.

A cikin bayaninsa ta shafin sada zumunta na Twitter, Ministan kananan hukumoni da karkara na kasar, ya ce suna canza wasu ka'idojin ne a kasar yadda zai kawo sauki da amfani wa dukkan jama'a.

Bangaren cin abincin maza a kasar Saudiyya

Idan za a tuna, kwanakin baya Yariman kasar, Mohammed ya kawar da yanayin shiga wuraren kallon fina finai da kuma bai wa mata 'yancin tuki a kasar.

Da yake Saudi Arabiya kasa ce wacce take bin ka'idojin addinin musulumci, za mu tsaya mu ga yadda sauran jama'ar kasar da kuma sauran duniya za su ce game da wannan canji.