A Gobe Za Ayi Zaben Rabin Wa'adi A Kasar Amurka

Manyan Jam'iyun Amurka Republican da Democrat suna kokawar samun rinjaye a zaben 'yan majalisar wakilai, dattawa da kuma wasu gwamnoni kasar, daza ayi gobe Talata.

‘Yan takarar da ke neman kujerun majalisar dokokin Amurka da manyan ‘yan siyasar kasar masu mara musu baya, za su yi amfani da yau Litinin a matsayin rana ta karshe wajen jan hankulan masu kada kuri’a, yayin da manyan jam’iyyun kasar ke kokawar ganin sun samu rinjaye a majalisar wakilai da ta Dattawa a zaben rabin wa’adi da za a yi gobe.

Shugaba Trump na burin ya ga cewar ‘yan jam’iyyarsa ta Republican sun ci gaba da rike rinjayen majalisun biyu, yayin da su kuma ‘yan Democrat ke kokarin su kassara wannan rinjaye.

A lokacin wani gangamin yakin neman zabe da yaje a jihar Georgia a jiya Lahadi, shugaba Trump ya yi gargadi ga magoya bayansa, wannan zabe shi zai nuna ko za mu ci gaba da ayyukan alheri da muka faro ko kuma za ku bar 'yan Democrat su ruguza tattalin arzikinmu da kuma makomarmu.

Yayin gangamin yakin neman zaben da ya halarta a Indiana a jiya Lahadi, domin marawa dan takarar Democrat Joe Donnelly baya, wanda ke neman kujerar Sanata, tsohon shugaban Amurka Barack Obama, ya yi kira ga masu kada kuri’a, da kada su bari ‘yan Republican su yi musu shigo-shigo ba zurfi.

A gobe Talata Amurkawa za su kada kuri'u domin cike gurbin dukkanin kujerun ‘yan majalisar wakilai 435 da kujeru 35 daga cikin 100 na majalisar Dattawa.