A Jahar Adamawa APC na Maida Martani, PDP na Kare Matsayin Ta

Murtala Nyako, gwamnan Jihar Adamawa

APC ta ce bita da kulli, PDP ta ce kyakkyawan manufa, talakawa na cewa da ma an hakura wa'adin mulkin Nyako ya kusa karewa.
Daga cikin 'yan majalisar dokokin jahar Adamawa ishirin da biyar, goma sha tara sun amince da matakin tsige gwamna Murtala Nyako da mataimakin shi Barrister Bala James Ngillari a jiya Laraba. Tuni dai jam’iyar APC da sauran talakawan jahar su ka fara maida martani kan wannan matakin tsige gwamna Nyako da mataimakin shi,

Jam’iyar APC ta maida martanin ne ta bakin kakakin ta Reverend Phineas Padio wanda ya ce yunkurin tsige gwamna Murtala Nyako ba wani abu ba ne illa bita da kulli:

Your browser doesn’t support HTML5

Martanin APC ta jahar Adamawa game da tsige gwamna Nyako.-0:53"


Su ma talakawan jahar Adamawa su na ci gaba da furta albarkacin bakin su akan matakin da majalisar dokokin jahar ta dauka na neman tsige gwamna Murtala Nyako da mataimakin shi Barrister Bala James Ngillari:

Your browser doesn’t support HTML5

Ta bakin Yakubu Baffa wani dan Adamawa kan tsige gwamna.-0:32"


A na ta bangare, majalisar dokokin jahar Adamawa ta kare matsayin ta da kuma matakin da ta dauka na neman tsige gwamna Murtala Nyako da mataimakin shi. Kakakin majalisar dokokin jahar Adamawa Ahmadu Fintiri ya ce babu wanda ya sa su, sun yi ne da kyakkyawan manufa:

Your browser doesn’t support HTML5

Kakakin majalisar jahar Adamawa ya na kare matakin da suka dauka.-1:03"


An yi ta samun takun saka tsakanin gwamnan jahar Adamawa Murtala Nyako da ‘yan majalisar dokokin jahar tun bayan da gwamnan ya cyi canjin sheka daga jama’iyar PDP mai mulki, ya koma jam’iyar APC ta hamayya.

Haka nan kuma yanayin siyasar jahar yayi zafi ne tun bayan da majalisar ta baiwa kwamishinan ‘yan sandan jahar umarnin kama wasu kwamishinoni hudu ya tsare su saboda sun ki gurfana a gaban majalisar su amsa tambayoyin ta game da yadda ake kashe kudaden gwamnatin jahar. Wakilin Sashen Hausa a jahar Adamawa Ibrahim Abdulaziz ne ya aiko da wannan rahoto.