A Jamhuriyar Nijar Ana Ci Gaba Da Mayarda Martani Akan Korar Tillerson

Rex Tillerson, sakataren harkokin wajen Amurka da Trump ya kora yana yiwa ma'aikatan ma'aikatarsa ban kwana

Gaf da dawowarsa daga nahiyar Afirka, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi waje da Sakataren Harkokin Wajen kasar kana ya nada shugaban CIA ya maye gurbinsa lamarin da ya ba kowa mamaki musamman kasashen Afirkan da Sakatare Rex Tillerson ya kai ziyara

A Jamhuriyar Nijar masana na ci gaba da yin tsokaci dangane da korar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yiwa Sakataren Harkokin Wajen kasar, Rex Tillerson.

Korar tana zuwa ne bayan da sakataren ya kammala ziyarar wasu kasashen Afirka da suka hada da tarayyar Najeriya.

Habib Mummuni sakataren kungiyar malaman makaranta cewa ya yi Donald Trump bai san makamin mulki ba. Ya ce Allah dai ya bashi mulki amma bai san kan mulkin ba. Injishi duk mutanen da suke tare dashi ya koresu daya bayan daya ba tare da yin wani laifi ba. Ya ce ko Amerikawa ma sun fara gajiya da salon mulkinsa.

A nasa ra'ayin magatakardan kungiyar ma'aikata reshen Konni Cuwada Yusuf Adamu yana ganin korar da Donald Trump ya ke yiwa ma'aikatan ba banza ba ne saboda mutanen sun san abubuwan da ya keyi, wato sun san sirinshi dalili ke nan yake korarsu.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

A Jamhuriyar Nijar Ana Ci Gaba Da Mayarda Martani Akan Korar Tillerson - 3' 11"