A Mexico Karin Farshin Man Fetur Ya Harzuka Borin Jama'a

Irin barnar da aka yi a Mexico

Tashing gwauron-zabi da farashin man fetur yayi a kasar Mexico ya janyo mummunar zanga-zanga da wasoson dukiyar jama’a a jiya a kasar, inda mutane ke ci gaba da jin jiki a sanadin karin farashin.

Tun ran 1 ga watan nan na Janairu, lokacinda gwamnatin kasar ta bada sanarwar karin kashi 20 cikin 100 ga farashin man fetur, mutane suka fara tada bore, suna toshe hanyoyin mota da hanyoyin zuwa gidajen saida man, da hana zirga-zirgar abubuwan hawa da kuma gudanarda tarukkan gangami iri-iri.

Yunkurin wawushe shaguna da aka yi a jiya Laraba dai ya sa ‘yan sanda sun kama mutane fiye da 200, a cewar ma’aikatar Harakokin Cikin Gida.

Wasu kungiyoyin ‘yankasuwa sun ce kantuna kamar 79 aka yi wa wasoson, aka kuma tilasta wa wasu shaguna 170 zama a rufe ala-tilas.