A Takaitawa 'Yan Sanda Yin Amfani Da Karfin Da Ya Wuce Kima - Dan Uwan Floyd

Philonise Floyd

A wani zama da ‘yan majalisar Amurka game da sauraron bayanai akan yin garambawul ga hukumar ‘yan sandan Amurka, kanin George Floyd, Ba’amurken nan bakar fata wanda ya mutu a hannu ‘yan sandan birnin Minneapolis, ya yi kira ga ‘yan majalisar da su amince a takaita yin amfani da karfi da ‘yan sanda ke yi akan farar hula.

A jiya Laraba Philonise Floyd ya yi wannan korafin a gaban kwamitin shari’ar majalisar wakilan Amurka a madadin yayansa.

A ranar 25 ga watan Mayu George Floyd ya mutu bayan da Derek Chauvin ya danne wuyansa da gwiwa har tsawon kusan minti 9 a yayin da Floyd ya yi ta magiya yana kiran mahaifiyarsa ya na kuma cewa bai iya numfashi.

Hoton bidiyon yadda lamarin ya auku ya janyo zanga zanga a fadin Amurka da kuma kiran a yi sauye sauye ga Fannin 'yan sanda.